30/08/2023
Wasu idan Account ɗinsu na Facebook ya shiga Restrictions ko kuma aka hanasu comment ko posting na tsawon wasu ƙwanaki wasu ma daga ƙarshe rufe account ɗin nasu akeyi musamman idan Account ɗin an dora shi akan tsarin tsaro na Two Step Verification, to idan mutum ya saɓa dokar Facebook ɗin s**an ɗauki mataki, ɗaukar matakin ne sai mutane sudinga zagin Mark Zukerberg shugaban kamfanin Facebook suna cewa shine ya rufe masu Accounts..😀
Wato akwai wani tsarin Algorithm da aka samar a manhajar Facebook ɗin wanda shine yake ɗaukar matakan rufe account na mutane ko kuma sanya masu wani takunkumi ko makamantansu. Waɗannan tsarukan suna Detecting “Spam posts/abused” based on "Machine Learning Algorithms," Automatically da zaran ka saɓa dokar Facebook ko akayi masu reports da yawa sai "ML Algorithm" through Natural Language Understanding Steps (NLP) ya hau bincike tareda “parsing” statements ɗin daya fahimci kalmomi ko bayanan da s**a taka dokar Facebook shi kuma wannan tsarin daganan kawai sai ya aikata abinda aka umarce shi da yayi da zaran ya samu waɗannan kalmomin da s**a saɓa ƙa'ida, wato kenan zai goge Account ɗin ko ya jefa Account ɗin Restrictions ko ya saka ma Account ɗin takunkumin yin Comments ko Posts da sauransu, duk komai zai iya faruwa bayan wannan tsarukan na Algorithms da aka tsara yayi detecting.
Dan haka lokacin da ake kulle maka Account ko ake hanaka Comment ko Posting, shugaban Facebook Mark Zukerberg bashida labari..😁
Allah Yataimaka..🙏
©engr arafat